This page is a translated version of the page Wikimedia Foundation elections/2022 and the translation is 92% complete.
Outdated translations are marked like this.

A lokacin zaɓukan Kwamitin Amintattu na 2022, ƴan takara biyu daga al'umma da ƙungiyoyi za'a zaɓe su domin aiki a Wikimedia Foundation Board of Trustees. Wannan shafin na ɗauke da bayanai game da zaɓukan Kwamitin Amintattu na 2022.

The elected candidates were:

You may also view the full results, including the outcome of each round of Single-Transferrable Vote.

Game da zaɓen

Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Wikimedia suke sanya ido game da ayyukan Gidauniyar Wikimedia. Amintattu na al'umma da amintattu da aka zaɓs sune ke samar da Kwamitin Amintattu. Kowane amintacce zai yi aiki na tsawon shekaru uku ne. Al'ummar Wikimedia suna da damar zaɓan amintattun da zasu wakilci al'umma da ƙungiyoyi. Ƴan takara biyu zasu shiga cikin Board of Trustees. Ɗan takarkaru da aka fara zaɓa su za'a ƙungiyoyi zasu tantance sannan daga ƙarshe al'umma su zaɓe su.

Ƙwarewar da ake nema da basira

Wikimedia wata fafutuka ce ta duk duniya kuma Kwamitin ta na neman ƴantakara daga farfajiyar al'ummar ta. Ƴantakara da suka fi dacewa da alaƙa da manufar Wikimedia kuma masu basira, girmamawa da kuma sanin al'ummar.

Kwamitin na son samun fasahohi da muryoyin da ba'a cika wakiltan su ba kuma masu muhimmanci a tafiyar. Dan cike gurbi da yin wakilci cikin Kwamitin mai tarihi na yanzu, Kwamitin Amintattun na burin ƙarfafa neman shiga cikin ta musamman ga waɗanda suke da ƙwarewa daga waɗannan yankuna: Afirka, Kudancin Asiya, Gabas da Kudu masu gabas na Asiya da Pacific, da kuma Latin na Amurka da Caribbean. Ƙwarewar da ake nema na yanki bawai buƙata bace, amma abu ne da zai bunƙasa ku. Akan ace tilas ne, waɗannan muhimman abubuwa ne da Kwamitin ke neman kowa ya kalla.

Kwamitin ya fahimci zai iya yiwuwa wasu ƴantakara daga yankunan da ba'a ba muhimmanci ba, zasu iya zuwa su bada damar samun mabanbantan al'umma akan wasu ƴantakaran daga yankunan da aka muhimmanta waɗanda basu duba tsarin rabo na daidaito. Ƴantakara su yaɗa yadda ƙwarewar su ta taimaka masu dan yaɗa gamuwar mabanbantan mutane, daidaito, da tafiya da kowa.

Dabaru

Fannonin ƙwarewa da Kwamitin ya nuna zai fi amfanar da sabbin amintattu ne dan su zo da:

  1. Dabarun gudanar da ma'aikata da kula
  2. Matakin fasaha ta kamfani da kuma/ ko bunƙasa samfuri
  3. Manufar jama'a da doka
  4. Kimiyyar bayanai ta zamantakewa, binciken manyan bayanai, da kuma koyon na'ura

Samu ƙarin koyo game da hangen da ake nema, ƙwarya da dabaru na ƴantakara zasu samu a wannan zaɓen a shafin Neman zama ɗantakara.

Zaɓen al'umma

Mambobi na al'umma suna da damar zaɓan amintattu guda biyu daga cikin ƴantakara shida da ƙungiyoyi suka fitar. Single Transferable Vote a SecurePoll wanda za'a yi amfani da shi wannan shekara.

Wasu mambobin al'umma sun lura akwai matuƙar ƙalubale a zaɓen ƴantakara a 2021. Adadin ƴantakaran yayi yawa sosai. Dan taimakawa yanayin gudanar da zaɓen ga mambobi al'umma, na'urar bada shawara ga zaɓen za'a kawo dan amfani da ita. Wannan zai zama kusan iri ɗaya da wanda aka yi amfani da shi a gudanar da zaɓen Movement Charter Drafting Committee.

Tsarin lokuta

April 2022
  • Amintattu zasu sanar da lokaci na tsara zaɓen da gudanar da zaɓen.
  • Kwamitin Zaɓe da tawagar Movement Strategy and Governance zasu fara aiki da ƙungiyoyi dan samar da Kwamitin masu Nazari.
Tsakiyar-Afrilu – farkon Mayu 2022
Ƙarshen Afrilu – farkon Mayu 2022
  • Kira ga Ƙungiyoyi da su samar da mambobi na Kwamitin masu Nazari.
Tsakiyar-Mayu – farkon Yuni 2022
  • Kwamitin masu Nazari su auna ƴantakara.
June 10, 2022 – June 17, 2022
  • Jagororin Affliates za su iya tura tambayoyinsu ga `yan takara kuma suyi upvoting tambayoyi a yanki majalisar MS na sirri.
June 18, 2022 – June 24, 2022
  • Lokacin da `yan takara za su amsa tambayoyi da kansu
Karshen Yuni
  • Kwamitin Nazari zai mika sakamon nazarinsa ga Jagororin Affliates ta hanyar email.
June 24, 2022 – June 30, 2022
  • Katagorin sirri na majalisar MS zai zama public, kuma `yan takara zasu iya bada amsoshinsu.
July 1, 2022 – July 15, 2022
  • Lokacin kaɗa kuri'ar ƙungiyoyi dan fitar da taƙaitattun ƴantakara.
Tsakiyan-Yuli
  • Wallafa taƙaitaccen jerin ƴantakara
  • Za'a buga ratings na Kwamitin Bincike a wiki.
Tsakiyar-Yuli – farkon Augusta 2022
  • Al'umma zasu yi tambayoyi ga ƴantakara sanarwa game da na'urar sshawara akan kaɗa kuri'a.
Tsakiyar-Yuli – tsakiyar-Augusta
  • Lokacin neman zaɓe da zai haɗa tattaunawar al'umma tare da ƴantakara.
August 19, 2022
August 23, 2022 – September 6, 2022
  • Lokacin zaɓe na al'umma
  • Buɗe na'urar shawara akan kaɗa kuri'a.
September 6, 2022 – September 21, 2022
  • Bincika sakamako da tabbatarwa daga Kwamitin Zaɓuɓɓuka
October 2022
  • Tabbatar da Amintattu

Shigar ma'aikatun da aka yi alaƙa


Ƙungiyoyi da aka yi alaƙa da su zasu yi zaɓe a wannan karon a Yuli dan zaɓan ƴa takara shida daga cikin dukkanin tarin ƴantakaran da ake da su. Duk wani ma'aikatan da aka yi alaƙa da su za'a ba su gurbin su yi zaɓe ɗaya. Wannan gurbin zaɓen za'a yi amfani da tsarin Single Transferable Vote. Ƙungiyoyin da aka yi alaƙa zasu tattauna tsakanin akan wani ɗan takara ne ƙungiyar suke son su zaɓa. Ƴantakara za'a ɗauka su akan jerin muhimmanci ne.

Jagororin Affliates zasu iya tambayoyi ga `yan takara domin su amsa. `Yan takara zasu iya bada amsa daga 24 ga Yuni.

Dan taimakawa a gudanarwan wannan zaɓen, za'a samar da Kwamitin masu Nazari.

Kwamitin Nazari

Dan rarraba ƙungiyoyi a yankuna da masu gudanarwa da zasu taimaka yin haka, duba Affiliates regional distribution for the Analysis Committee

Kwamitin masu Nazari an samar da shi ne daga ƙungiyoyi a ƙarshen Afrilu da Mayu. Kwamitin masu Nazarin na ƙunshi da wakilai 9 na ƙungiyoyi (ya haɗa da chapters, user groups, da thematic groups) daga yankuna dake cikin fafutukar. Ɗaya daga kowane:

  • CEE (Tsakiya da Gabashin Turai);
  • ESEAP (Gabas da Kudu-maso-gabas din Asiya, tare da yankin Pacific);
  • Yankin Saharar Afirka
  • Latin America da Caribbean;
  • MENA (Gabas ta tsakiya da Arewacin Afrika);
  • Amurka ta Arewa (USA da Canada);
  • Arewaci da Yammacin Turai
  • Asiya ta Kudu;
  • ƙarin ɗaya daga thematic affiliates.

There was no representative from the Northern and Western Europe or South Asia.

Tsarin gudanarwan zaɓen Kwamitin masu Nazarin ƙungiyoyi ne zasu tanadar da su, tare da taimakon Elections Committee da kuma Movement Strategy and Governance team kamar yadda aka buƙata.

Kwamitin masu Nazari zai kintace ƴantakaran akan matakin ƙwarewa da samun mabanbantan al'umma, daidaito da shigar da sanya kowa wanda Kwamitin Amintattu suka raba. Kwamitin masu Nazarin zasu yi amfani da sanarwan ƴantakara da suka amsa a cikin neman shigar su dan auna ƴantakaran. Kwamitin masu Nazari zasu auna ƴantakara akan ma'aunin zinari/azurfa/tagulla. Wannan ma'aunin zai yi amfani dan samar da masaniya ga ƙungiyoyin da aka yi alaƙa da su a sanda suke tsara zaɓen su. Bayanai akan kintacen kowane ɗan takara ba za'a yaɗa ba.

Bayan an zaɓa ƴan takara shidan lokacin gudanar da zaɓukan ƙungiyoyin da aka yi alaƙa da su, matakin kowane ɗan takara da aka zaɓa za'a wallafa dan sanar da zaɓin al'umma. Wannan tsarin na ƙoƙarin samo mafi dataccen tsakanin samun yaɗa bayanai mai amfani da taƙaita kuzarantarwa ga ƴantakara mara amfani.

Zaɓaɓɓun mambobin kwamiti

Mambobin Kwamitin masu Nazari
Yanki Wakili
CEE (Tsakiya da Gabashin Turai) Mehman97 (talk meta edits global user summary CA)
ESEAP (Gabas, Kudancin Asiya, da Pacific) GDHFang (talk meta edits global user summary CA)
Yankin Saharar Afirka Dnshitobu (talk meta edits global user summary CA)
Latin America da Caribbean Superzerocool (talk meta edits global user summary CA)
MENA (Gabas ta tsakiya da Arewacin Africa) علاء (talk meta edits global user summary CA)
Amurka ta Arewa Megs (talk meta edits global user summary CA)
Yammaci da Arewacin Turai
SAARC (Asiya ta Kudu)
Thematic Affiliates Joalpe (talk meta edits global user summary CA)

Hanya

Kwamitin Bincike ya yi aiki daga ƙarshen watan Mayu zuwa tsakiyar watan Yuni. Ana iya samun cikakkun bayanai game da tarurrukansu da tsarinsu akan Tattaunawar Kwamitin Nazari.

Kwamitin zaɓen hukumar da kwamitin zaɓe sun ɓullo da wani tsari na ma'auni don kwamitin nazari don tantance ƴan takara da su. Wakilan kwamitin nazari sun tantance ƴan takara ɗaya-ɗaya. Masu Gudanar da Dabarun Motsawa da Gudanarwa guda biyu ne kawai waɗanda suka goyi bayan tsarin sun sami damar samun waɗannan maki guda ɗaya.

Sake Duba