Zaɓukan Gidauniyar Wikimedia/2022/Kaɗan ƙuri'ar Al'umma
Outdated translations are marked like this.
Zaɓen 2022 na Kwamitin Amintattu za'a fara daga ranar 23 ga watan Agustan shekara ta 2022 zuwa ranar 6 ga watan Satumba shekara ta 2022.
Mambobi daga al'ummun Wikimedia na da damar zaɓar ƴan takarkaru biyu na zangon shekaru uku. Wannan shafin ya ƙunshi bayanai akan yadda za'ayi zaɓen,cancantan mai kaɗa ƙuri'a da FAQ.
Zaɓi
Idan ka cancanci ka jefa ƙuri'a:
- Karanta Jawaban ƴan takara kuma ka ga maki da Kwamitin masu bada Shawara suka bayar akan ɗan takara
- Karanta candidates’ answers to the questions posed by the Affiliate Representatives
- Watch the videos recorded by the candidates answering 6 questions from the community; there is also a text version, including additional questions from the community.
- Yi amfani da Election Compass ya taimaka maka wurin tunanin akan wanda ya dace ka zaɓa (based on answers to 15 additional community-sourced questions).
- Yanke shawarar wani ɗan-takara zaka goya baya.
- Je ka wurin kaɗa ƙuri'a a shafin SecurePoll.
- Bi dokokin gudanarwa da yake wancan shafin.
Yadda ake jefa ƙuri'a
'A kasa akwai wasu muhimman bayanai da zasu tabbatar da cewa zaben ku ya tafi dai-dai. A tabbata an karanta wannan sashin da kyau kafin kuje jefa kuri'a.'
- Wannan zaɓen na amfani da tsarin Single Transferable Vote. Bayanin yadda ake gudanar da lissafin tsarin na nan a nan.
- A shafin jefa ƙuri'a, mai kaɗai kuri'a zai ga jerin akwatuna masu saukowa. Mai kaɗai kuri'a zai jera ƴantakara a bisa “Zaɓin sa na 1” (mafi soyuwa) zuwa “Zaɓinsa na 6” (ƙarancin soyuwa).
- Farawa daga sama, mai kaɗa ƙuri'a zai jera ƴantakara da yaga yafi dacewa a zaɓa. Ƴan takarar da kuma mai kaɗai kuri'a yake ganin basu da dacewa sosai a zaɓa zai sanya su daga ƙasan jerin sa.
- Mai kaɗa ƙuri'a zai iya tsayawa da jera ƴantakara akowane lokacin yayin gudanar da zaɓen. Ga misali, cikin ƴan takara 6, mai kaɗa ƙuri'a na iya kawai jera ƴantakara 4 da suka fi dacewa kuma ya ƙyale sauran 2.
- Ana son a jera ƴantakara ba tare da tsallaken layi ko lamba a tsakani ba. Tsallake lamba zai sanya a samu matsala wurin zaɓen.
- Mai zabe ba zai jera sunan ɗan-takara fiye da sau ɗaya ba. Jero sunan ɗan-takara ɗaya fiye da sau ɗaya zai jawo samun kuskure.
- Mutane zasu iya sake kaɗa kuri'a a zaɓen. Zai goge ƙuri'ar da suka kaɗa na baya. Zasu iya yin hakan ko sau nawa suke so.