Wikimedia Foundation elections/2021/Candidate Requirements/ha
The election ended 31 Agusta 2021. No more votes will be accepted.
The results were announced on 7 Satumba 2021. Please consider submitting any feedback regarding the 2021 election on the elections' post analysis page.
Zaɓen amintattun ya haɗa da tsarin Kwamiti na Wikimedia Foundation aikin da za'a kula. Aikin amintattu akan tunani, ƙwazo, da sanin yakamata, da kular da masu hikima suke aiki da shi. Wannan aiki na kula zai haɗa cikakken kula a wurin zaɓen mutane da zasu yi aiki a Kwamitin. Irin waɗannan mutane kada su kawo waɗanda basu cancanta ba.
2021 Board Elections |
Main Page |
Candidates |
Voting information |
Single Transferable Vote |
Results |
Discussions |
FAQ |
Questions |
Organization |
Translation |
Documentation |
Ƴantakara su karanta Ƙaramin littafin Kwamiti na Wikimedia Foundation kuma suyi nazari akan a dokance nauyin da aka ɗaura wa amintattu da ayyukan da zasu yi kafin su nema zama ƴantakara.
Ayyuka da nauyi amatsayin ƴan Kwamitin Amintattu
Kwamitin amintattu suke lura da ayyukan da Wikimedia Foundation ke gudanarwa. Amintattu nagari suke samar da ayyukan gudanarwa masu kyau ta hanyar CEO/Executive Director kuma ba akai tsaye ba, ma'aikata. Basu ne ke kula da ma'aikatar ba a ayyukan yau da kullum. Kwamitin na aikin akan abinda ya ƙunshi samar da matsaya, bibiya, da shugabanci.
Waɗannan nauyi sun haɗa da:
- Cimma matsaya ta dubi ga tsari da burin ma'aikatar da dokokinta;
- Lura da yadda ayyukan Wikimedia Foundation, riski da take ɗauka, kuɗaɗe, da kuma yadda take bin ƙa'ida;
- Bayar da shawara ga CEO/Executive Director da manyan ma'aikata ta hanyar amfani da ƙwarewa data dace; da
- Tattaunawa da al'umma Wikimedia akan ayyukan kwamiti ɗin da nauyin dake kansu.
Amintattu ke tabbatar da nagarta da ɗa'a na ma'aikatar. Kuma sune ke sanyawa da kawo banbantaka acikin kwamitin. Amintattu a koda yaushe dole suyi aiki akan cigaban Wikimedia Foundation. Za'a zaɓe amintattun ne ta hanyar zaɓe daga al'umma, amma a sanda suka zama daga cikin kwamitin, sun fita daga zama wakilai na al'ummu.
Sama ƙarin bayani game da ayyukan Kwamitin Amintattu acikin Ƙaramin littafin Kwamiti na Wikimedia Foundation.
Cancanta
Ƴantakara dole su cika ayyukan kwamiti da abinda zasu gudanar. Wannan ya haɗa da neman sani cikin abubuwan da suka dace, samar da matsaya, da halartar mitin na kwamiti ɗin. Abinda ake nema ga masu neman takara sune iri ɗaya dana masu zaɓe da waɗannan ƙarin bukata:
- Dole kada ku zama an taɓa kulle ku akan laifi mai ƙarfi wanda ya danganci rashin gaskiya ko damfara;
- Dole ya zama ba'a taɓa tsige ku daga muƙamin ku ba a ma'aikata ta sakai ko kamfani saboda rashin gudanarwa maikyau ko rashin ɗa'a;
- A lokacin gabatarwa ko yin zaɓe, kar yazama an kure ku ko kulle ku daga kowace Wikimedia project na tsawon kwanaki 30 ko fiye da haka;
- Idan kawai kun cika cancantar yin zaɓe ne amatsayin edita: Edit ɗin ku na farko ya kasance kunyi tun a 9 Yuni 2019;
- Dole ku bada asalin sunan ku a cikin neman buƙatar ku ta zama ƴantakara;
Ba zai zama dole ku riƙe muƙami ba a Kwamitin Amintattun ba a ƙarƙashin sunan da ba'a san waye ba saboda sanayyar kowa a Kwamitin Amintattun zai kasance ne a bayyane ga kowa.
- A ƙalla dole ku kai shekaru 18 kuma a dokance a ƙasar ku;
- Dole ku bayar da tabbaci na tabbatar da kanku da shekarar ku ga Wikimedia Foundation; da kuma
- Idan an zaɓe ku ko naɗa ku acikin Kwamitin Amintattu, dole ku sauka daga kowane irin bod da kuke ciki, shugabanci, ko muƙami na biya a Wikimedia Foundation, chapters, thematic organizations, da user groups.
Ƙa'idojin nema
- Kada ku bada bayyanan ku na neman takara dan a goya maku baya ko ku kai su wasu wurare, kuma kar a sanya su a slate tare da wasu ƴan'takaran.
- Za'a amsa buƙatun neman takara daga 00:00 9 Yuni 2021 (UTC) zuwa 23:59 29 Yuni 2021 (UTC). Zaku kawai iya canja buƙatun ku ne har kwanaki uku bayanan kun tura buƙatar, ko kuma a ƙarshen kulle karɓar takarar a 23:59 29 Yuni 2021 (UTC). Za'a amince da ƙananan kura-kuran rubutu ko fassara idan aka fita a waɗannan lokuta. (Duba bayani akan neman gyaran bayanai.)
- Dole masu neman takara su bada tabbacin su su wanene ga Wikimedia Foundation kafin 23:59 29 Yuni 2021 (UTC). Mamba daga cikin Kwamitin Zaɓe zai tuntuɓe ku akan haka bayan kun tura buƙata.
Ƴantakara da suka kasa cimma waɗannan buƙatu har aka kulle za'a zubar da su.
Bayar da tabbacin kanku ga Wikimedia Foundation
Ƴantakara dake neman wannan matsayi dole su bayar da tabbacin kansu da na shekarar mafiya rinjaye amatsayin ƙa'idar cimma matsaya. Idan an sami copy na ɗaya daga cikin wannan abubuwan an cika ƙa'idar:
- Driver's license
- Passport
- Other official documentation indicating real name and age
Wannan za'a iya bayar da su ga Wikimedia Foundation ta hanyar imel a secure-info wikimedia.org.
Idan kana ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun ƴan'takara, Wikimedia Foundation na iya neman ƙarin bayanai dan gudanar da binciken bayan gida kafin naɗa ku zuwa Board.
Yadda zaku tura takarar ku
Idan kun cancanta zaku iya Neman zama ɗan takara.