Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Wikimedia/Dubiya
Gidauniyar Wikimedia
Kwamitin Amintattu
Gidauniyar Wikimedia yana da Kwamitin Amintattu da zai kula da dabarun Gidauniyar Wikimedia. Sun amince da abubuwan da Gidauniyar ta fi ba da fifiko da albarkatun da ake buƙata don isar da su. Ba a biyan membobin hukumar kuɗin aikinsu kuma masu aikin sa kai ne - suna haɗa ra'ayoyi da ra'ayoyi daban-daban ga yanke shawara. Kuna iya ba da ra'ayin ku kan wanda ke cikin hukumar ta hanyar jefa kuri'a. |
Ayanzu akwai kujeru 16 a Kwamitin: |
|
Ana zaɓar amintattun da aka zaɓa ta hanyar tsarin bincike na duniya. Suna shiga hukumar da zarar Kwamitin Amintattu da ’yan takarar sun gamsu an samu daidaiton juna. |
Bincika ƙarin bayani game da Kwamitin Amintattun a https://w.wiki/yY9. |