Makarantan GLAM/Tambayoyi

This page is a translated version of the page GLAM School/Questions and the translation is 100% complete.

Wannan shafin na kunshe da tambayoyi da akayi amfani dasu wajen sharar fage da kuma ta tattaunawa. Zaku iya taimaka wa ta hanyar fassara su zuwa harsunan ku. Hakan zai taimaka wajen yaɗa wannan bincike zuwa fahimtar ku na gargajiya. Har ila yau zamu iya bada shawarwari kan canje-canje da Za'a iya wa tambayoyin binciken ta hanyar yin tsokaci a shafin hira.

Gabatarwa

Da zartar ka amsa waɗannan tambayoyi to ka/kin yarda a wallafa bayan an ku a CC0 at https://meta.wikimedia.org/wiki/GLAM_School/Interviews. Amsoshin zasu kasance cikin sirri face ka/kin amince da cewa a wallafa su da sunan ka/ki. A yayin da kuka adana wannan fom din, za ku sama ma hada da zai kai ku shafin da zamu iya gyara amsoshin ku. Ta haƙan, b a sai lallai kun kammala wannan bincike ba a lokaci guda ba. Zamu iya ƙara wasu tambayoyin a lokacin da ake tsakar gudanar da binciken, sannan zamu sanar wa duk wanda ya amsa tambayoyin akan sabbin sauye-sauye.

Da zartar ka amsa tambayoyin to ka/kin ba u damar adana adireshin ka/ki na email da kuma amsoshin ku. Za'a adana su ne kawai na tsawon lokacin binciken. Wanda Za'a riqa riska akan wannan bincike ita ce Susanna Ånäs at AvoinGLAM, susanna.anas@gmail.com, https://www.avoinglam.fi/.

Zamu iya karanta tambayoyin sannan ku taimaka wajen fassara su zuwa harsunan ku a Special:Translate/GLAM School/Questions.

Email *

Ta yaya kuke so ku taimaka wa wannan binciken?

  • Zan so in ta aji lokacin intabiyu
  • Naji daɗin maida bayanai ta hanyar wannan binciken

Menene ma yan ra'ayoyi ku dangane da tallafawa masu bada gudummawa da kuma ƙwararrun GLAM a wajen bada gudummawa ga buɗaɗɗun muhalli da kuma shafi an Wikimedia.

A taimaka a amsa wannan tambaya ko da daga baya ya kasance ana so a amsa tambayoyi na daban da mu, ko da a takaice ne.

Sunan ka/ki

Amsoshin sirri *

  • Ina so in tsaya a boƴe
  • Za'a iya dangantani da amsoshi na

Shin kana bayyana kanka a matsayin

'A yi bayanin ra'ayoyin a shafin https://meta.wikimedia.org/wiki/GLAM_School/Definitions.

  • Ƙwararrun GLAM
  • Wakilan Open GLAM
  • Masu bada gudummawa a GLAM da Wiki
  • Masu bunƙasa wa da kuma ƙwararrun kimiyya
  • Masu koyarwa
  • Masu baiwa
  • Masu tsara dokoki
  • Masu zartarwa
  • Wasu daban:

Masana'antarku ko kuma Ƙungiyoyin al'umma ku

Shin kuna bayyana Masana'antarku ku ko kuma al'umma ku a matsayin

An bayyana ra'ayoyi a shafin https://meta.wikimedia.org/wiki/GLAM_School/Definitions.

  • Rassan Wikimedia
  • Sashin Creative Commons
  • Sashin ko kungiyar watsa ilimi kyauta
  • Sashin ko kungiyar OpenStreetMap
  • Wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu
  • Archive
  • Wuraren tarihi ko kuma galleria
  • Labrari
  • Kamfani in watsa shirye-shiryen da labari
  • Ma'akatun ilimantarwa ko ayyuka
  • Ƙungiyoyin gwamnati
  • Masu samar da takanoloji
  • Ƙungiyoyin da ke da ra'ayi wanda ba'a yi rijistansu ba
  • Sauran sana'oi
  • Masu bada tallafi ko gidauniya
  • Wasu daban:

Ƙasa

Wa suka fi dacewa?

Wasu mutane ne ko kungiyoyi suka fi dacewa da su kasance wadanda zasu rika bada gudummawa ga abubuwan gado na tarihi zuwa ga sauran muhalli? Ta yaya zai fi dacewa a saka su cikin tsarin ko kuma a kara musu karfin gwiwar yin aikin.? Ta yaya zamu sanya GLAM ya zamanto sashi mai muhimmanci na adana abubuwan tarihi na duniya? Ku kara fahimtar ku dangane da kungiyoyin da aka ambato, Zaku iya tsallake ko wanne sashe, ku kara sabon bayani, ko kuma ku dawo don inganta amshoshin ku a mataki na gaba.

Kwararrun GLAM

Ta yaya ne kwararren ma'aikacin GLAM zai samu ribar bada gudummawa ga wannan harkokin? Wadansu abubuwa ne wannan harkokin ke bukatar warware wa? Menene abubuwan da kowanne kwararre ke nukata ya yi don kafa muhawara mai karfi a yankinsu don zama budadde? Wadansu salon oyarwa ne zasu fi dacewa da nasu yankunan.

Al'ummar Open GLAM

Ta yaya ne al'ummomi daban-daban na GLAM suke saduwa, sannan ta yaya zasu fi samun daman cudanya da juna? Wadansu tsarukan duniya ne zasu yi aiki, sannan kuma wadansu cudanya na gargajiya ne tsakanin hanyoyin sadarwa zasu fi zama mafi a'ala.

Al'ummomin GLAM-Wiki

Mutane na daga kungiyar Wikimedia wadanda ke aiki da bada gudummawa kayan GLAM da abokan huldarsu, a matsayin masu bada gudummawa, ma'aikatan gida na Wikimedia, masu habaka harkokin yanar gizo da kuma duk wanda ke da alaka da wannan kungiya,

Wasu masu bada gudummawa ga Wikimedia

Ta yaya zaifi dacewa ayi mu'amala da kungiyoyin al'ummomin Wikimedia sannan kuma a sanya masu bada gudummawa ga harkokin GLAM da kara karfafa su don su zamo abokan hulda, sannan kua su hada kai wajen yin ayyuka daban daban don amsar gudummawar GLAM da hannu biyu-biyu.

Kayan al'ummomi

Ta yaya za'a fi sanar da kungiyoyin da basu da lasi masu kula da kayan tarihi, kananan al'ummomi, kungiyayi adana kayan gado, kungoyi masu ajiya da makamatan su zakan damammaki da open ecosystem zasu iya badawa?

Masu bunkasa Takanoloji

Ta yaya za'a inganta hanyoyin zama mai bada gudummawa na musamman ga open ecosystem? Ta yaya za'a tallafawa al'ummomi da kungiyoyin masu bada gudummawa da kuma abokan huldar GLAM da suke aiki tare? Ta yaya za'a daidaita ayyukan da suke da karancin kayan aiki da kayan aiki da suka dace? Dauki kanka/kanki misali: Wani irin gudummawa zaka iya badawa, sannan kuma me kake bukata?

Yan Makaranta

Masu bincike da daliban ilimi da kuma sauran shirye-shirye na al'adu da mutane, adanawa, sadarwa, fasaha, zane-zane da dai sauransu.

Masu Koyarwa

Sauran masu koyarwa, kamar malaman ilimin boko, ko kuma koyarwa na gargajiya, kwararru a harkokin koyarwa.

Masu Kirkira

Masu kirkira, zane, mawaka da dai sauransu daga kowanne sashi. Ta yaya Budaddun Hanyoyin isa zuwa kayan gado na tarihi zai bunkasa ayyuka masu kirkira? Ta yaya masu kirkira zasu fahimci open license a matsayin damar su?

Masu kafa dokoki

Menene abubuwan da masu kafa dokoki zasu iya yi dangane da kayan gado na tarihi ga Open Access? Ta yaya zasu kasancewa cikin shiri kuma su ga amfanin sa? Ta yaya zasu fi bada gudummawa wajen muhawara da kuma mu'amala da al'ummomi daban-daban na GLAM?

Kara sashin da babu sannan kuma ka fadi dalilin yin hakan

Zurfafa ayyuka

Yi bayanin ta yaya mutum zai iya bada gudummawa da kayan tarihi na kyauta a wannan sashin na open ecosystem.

Fadi sunan mutumin (ko mutum)

Tana iya zama kai, wani wanda ka sani ko kuma wani da kake tsammani.

Bada Labarin

Yi tunaninn yadda labarin ya kasance: me yasa wannan mutumin ya kara fahimtar tsarin bada gudummawa da kuma amfani da kayan kyauta na al'umma, menene matakai na farko da ake bukata, wani irin cikas za'a iya samu a kan hanya, sannan kuma ta yaya za'a iya magance su. Tana iya zama kai, wani wanda ka sani ko kuma wani wanda kake tsammani. Bada bayanin asalin wannnan mutumin: aikin shi, kwarewarshi a aiki, ra'ayoyi da makamantansu.

Zaku iya kara mahadar yanar gizo ta da hoto

Sanya hoto da ke dauke da bayanan labarin ku

Kayan koyo

Akwai bukatar raba kayan koyarwa matuka. Duk da haka, har yanzu ba'a gama fahimtar yadda za'a tsara su ba ko kuma a ina ne za'a ajiye su ba.

Wadansu kalan kayayyaki ne zafi dacewa a samar?

Fadi wanene kafi samun sa da muhimmanci, ko kuma menene zaka so a samar, ko a inganta, ko kuma gargajiyantar kuma a bunkasa kyawunsa. Zaku iya tunanin sashin koyarwa, bidiyoyi, podcast, kafar sadarwa, yanar gizo, jerin bayanai, labarin asalin mutane, kwas-kwas, MOOC, kalanda da dai sauransu, don bada misalai.

Wadansu darussa ya kamata su kunsa?

Wadansu darussa ne kake gani sune mafi muhimmanci a gareka? Zaka iya tunanin darussa dangane da halayya da kuma fasaha, da kuma wasu abubuwan dake tsakaninsu.

Ya kake gani tsararren wurin ko kayan koyarwa zasu kasance?

A wace kafa ce za'a iya samar da wannan shiri kai tsaye? Menene abubuwan da ake bukata, misali wajen isarwa ko kuma fassarori? Ya kuma batun harkokin mu'amala, bidiyo, syllabi da dai sauransu?

Menene za'a kirkira sannan kuma da menene za'a iya hade su?

Ba sai an kara kirkirar tayoyi ba. Ta yaya za'a bunkasa abun da yake nan tuni don yaduwa a yanar gizo, sannan kuma menene za'a sake kirkira don mamaye tsohon? A taimaka a kawo jerin kayayyakin da ake tunanin zasu yi amfani idan aka raba.

Tsari

Ya ake ganin kwas ko kuma tsarin bita zai kasance don koyon ayyukan GLAM? A kula da kungiyoyin masu bada gudummawa a amsoshin ku, misali idan kana magana akan masu bada gudummawa ko kuma kwararrun ma'aikatan GLAM.

Yaya tsarin bitar GLAM zai kasance?

Menene darussan da zasu kasance a cikin tsarin bitar GLAM? Menene abubuwan da kowa yafi bukata ya fahimta dangane da GLAM, wasu hanyoyin rikitarwa ke ciki?

Jagorancin salon koyarwa

Wadansu kalan jagoranci ya kamata a baiwa shirye-shiryen koyarwa don amfanin tsarin duniya ko kuma masu bada gudummawa na gargajiya, kamar kwasa-kwasai, MOOCs ko kuma ajujuwan kwararru, sannan ga wanni kungiya ake hari? Ta yaya za'a iya maida su a gargajiyance ko kuma riskar su a sassa daban daban?

Koya na kai da kai

Ta yaya za'a iya sarrafa wannan ilimin koyarwar don koyon kai da kai? Shin za'a rika amfani da ayyukan OER don hakan?

Kwarewa

Wadansu darussa ne ke bukatar kwarewa ko kuma tabbatar da ilimin aiki don harkokin kayan tarihi na kyauta ga al'umma, sannan da kuma amfanin wadannan shafukan da kayan aikin? Me yasa kwarewa ke da muhimmanci a wannan sashin? Wadansu irin kwarewa ake tunanin samun: shaidar kammala karatu, baje, jerin nasarori...

Ayyukan samfuri da nazarin shari'a

Bari mu san game da samfuran ku masu nasara don koyo, koyarwa da ba da shawarar al'amurran da suka shafi GLAM

Zaka iya bayanin labarin nasara guda daya ko fiye da hakan. Fadi dalilin da yasa kake tunanin cewa wannan labari na nasara ne. Kuma ka/ki yada idan wani daban ya samu akasarin abun da ka samu.

== Sabbin tsaruka don samarwa-na hadin gwiwa

Ayyukan GLAM sun warware lamura musamman idan aka hada su da suaran kayan koyarwa da kuma adana kayan gado na tarihi. Yi tunani akan wadannan tasgwaro sannan kuma kayi tunanin me aka rasa acikinsu.

Yi bayanin sabon tsari don koyo tare

Yi tunanin wurare na daban, cakuda sauran kungiyoyin masu bada gudummawa da wurare, canza matsayi, amfani da labarai daban daban da kuma lokuta.

Abubuwan da ke faruwa

Al'ummar GLAM na fuskantar sabbin kalubale dangane da bude kofa ga kayan tarihi. Misali, wasu gidajen tarihi suna shirye su sadar da tarin tarin su maimakon buɗe su don sake amfani da su. Ana ɗaukar masu haƙƙin da mamaki lokacin da abubuwan da suka fitar a bayyane ake amfani da su don horar da AI. Al’ummomin ’yan asali suna jin an zalunce su idan aka yi amfani da iliminsu na gargajiya kyauta, tunda ba a kiyaye shi ta hanyar haƙƙin mallaka.

Wane batutuwa ne masu tasowa kuke so ku haskaka?

Rubuta game da ɗaya ko fiye. Idan zai yiwu, ba da ɗan bayanan baya.

Wane hanyoyi ne masu ma'ana don tattauna batutuwan da suka kunno kai a cikin al'ummar GLAM?

"Wane irin al'umma, dandali da tsare-tsare ne zai fi sauƙaƙa tattaunawa mai fa'ida da kuma ba da shawarar mafita ga batutuwan?"

Wanzuwa, rashin nuna bambamci da kuma shigarwa =

Ta yaya za'a bi a sanya DEI cikin tsarin harkokin GLAM sannan kuma da wajen ilimin koyarwa?

DEI acikin jerin darussan koyo na bada gudummawa ga GLAM

Ta yaya za'a cike gibin dake cikin kayan GLAM? Ta yaya za'a fuskanci kuma a tafi tare da wadannan kayyaki na al'ummomi?

Harkokin DEI a GLAM

Ta yaya za'a daidaita tsakanin budewa da kuma kare martabar abubuwa masu muhimmanci na musamman al'ummomi masu kananan kima? Wadansu kalan jagoranci ake bukata don aiki da kaya masu muhimmanci? Ta yaya za'a sanar da masu bada gudummawa da abokan aiki akan kayayyaki masu muhimmanci, sannan ta yaya za'a rika mu'amalantar su a lokutan amfani a ayyukan yau da kullum?

DEI a matsayin sashin kayan koyarda da zane-zane

Ta yaya za'a dauki salon kwarewa daban-daban a wajen samar da kayan koyarwa. Ta yaya za'a shirya kayan al'adu da kuma yaruka daban-daban?

Kirkira kungiyar al'umma

Ta yaya al'ummomi daban daban daga fadin GLAM zasu yi aiki matsayin gangar jiki guda daya?

Kafafen sadarwa

Wadansu kafafe ke nan, menene iyakokin su, sannan ta yaya za'a iya riska iyakokinsu?

Taro

Wani taro ne zai yi marhaba da masu bada gudummawa daga sassa daban-daban, a inane wadannan kungiyoyi zau hadu? Ta yaya za'a iya riskar masu bada gudummawa a wannan taron?

Sauran bayanai

Wadansu sauran hanyoyi ne ku ke tunanin zai kara karfafa samar da kungiya a tsakanin tagwaro da dama?

Tasiri

Wadansu ire-iren tasiri ne ayyukan GLAM zasu bi don isa ga masu sanya hannun jari da dama? Ta yaya za'a tattara wadannan shaidu kuma a sadar da su?

Tasiri

Wadansu kalan tasiri ayyukan GLAM suke da shi? Wani irin sako suke bukatar isarwa ga masu siyan hannun jari daban daban?

Kintatawa

Mai ake buktar a kintata sannan saboda wani dalili ne hakan? Ta yaya za'a iya sadar da ita?