Zaɓen gidauniyar Wikimedia/2024/Sanarwa/Dokokin fakitin bita - gajere

This page is a translated version of the page Wikimedia Foundation elections/2024/Announcement/Rules package review - short and the translation is 100% complete.

Yi bita tare da bayar sharhi a kan ƙunshi na zaɓin ƙa'idodin Hukumar Amintattun Gidauniyar Wikimedia Foundation ta shekarar 2024

Za ku iya samun wannan saƙon da aka fassara zuwa ƙarin harsuna akan Meta-wiki.

Zuwa ga kowa da kowa

Da fatan za a yi bita kuma ku bayar da tsokaci kan ƙunshi ƙa'idodin zaɓen Hukumar Amintattu ta Wikimedia Foundation daga yanzu har zuwa 29 ga Oktoba 2023. Kunshin ƙa'idodin zaɓin ya dogara ne da tsoffin juzu'in Kwamitin Zaɓe kuma za a yi amfani da shi a zaɓin Kwamitin Amintattu na 2024. Bayar da maganganun ku a yanzu zai taimaka musu wajen samar da tsari mai santsi, mafi kyawun zaɓin hukumar Ƙari a kan shafin Meta-wiki.

Mafi kyau,

Katie Chan
Shugaban kwamitin zaɓe