VisualEditor/Newsletter/2020/July/ha
Labarai akan Editin na 2020 #3
Read this in another language • Subscription list for this multilingual newsletter
Shekaru bakwai da suka wuce a wannan watan, kungiyar editoci suka bayar da ayi editin ta hanyar zahiri ga yawancin editocin wikipedia. Tun wancan lokaci, editoci sun cimma nasara babba:
- Fiye da miliyan 50 na editin ne akayi ta amfani da hanyar editin ta zahiri akan komfuta.
- Sama da miliyan 2 na sabbin mukaloli aka kirkira ta hanyar editin na zahiri. Sama da 600,000 na wadannan mukalolin an kirkire su ne a 2019.
- Editin ta zahiri ya cigaba da shahara. Yawan adadin editin da akayi ta hanyar editin ta zahiri ya karu a duka shekara tun da aka fara shi.
- A 2019, kashi 35% na editin daga sabbin editoci (editoci wadanda suka shiga akwatin su da ≤99 edit) sunyi amfani ne da editin ta zahiri. Wannan adadin ya karu a kowace shekara.
- Kusan miliyan 5 na edit din kan wayar hannu anyi sune tare da hanyar editin na zahiri. Yawancin wadannan edit din anyi sune tunda kungiyar editoci suka fara inganta editin ta zahiri na wayar-hannu a 2018.
- A 17 Nuwamba 2019, edit na farko daga sararin samaniya anyi sane daga hanyar edit din zahiri ta wayar-hannu. 🚀 👩🚀
- Editoci sunyi fiye da miliyan bakwai na edit acikin 2017 ta hanyar wikitext editin, wanda ya hada da fara sabbin mukaloli 600,000 aciki. Hanyar editin din Wikitext na 2017 shine Editin na zahiri da akayi ta yanayin wikitext. Zaku iya aiwatar da samun sa a preferences dinku.