Zaɓukan Gidauniyar Wikimedia/2022/Sanarwa/An soma kaɗa ƙuri'a na Al'umma a Zaɓen Kwamitin Amintattu na 2022

Outdated translations are marked like this.

An soma kaɗa ƙuri'a na Al'umma a Zaɓen Kwamitin Amintattu na 2022

Kuna iya samun wannan saƙon an fassara zuwa ƙarin wasu yaruka akan Meta-wiki.

Barka kowa da kowa,

Lokacin kaɗa ƙuri'ar al'umma a Zaɓen Kwamitin Amintattu na 2022 yayi. A nan akwai wasu muhimman bayanai da zasu taimaka maku samun bayanan da kuke buƙata dan kaɗa ƙuri'a:

Idan ka shirya kaɗa ƙuri'a, kana iya zuwa shafin kaɗa ƙuri'a na SecurePoll dan kaɗa ƙuri'a yanzu. Kana iya kaɗa ƙuri'a daga 16 zuwa 30 ga Augusta, 2022 23:59 UTC. Dan ganin ko ka cancanci kaɗai ƙuri'a, ku ziyarci shafin bayanin cancantan mai kaɗa ƙuri'a.

Da alkhairi,

Tsarin Gudanarwa da Shugabanci (Movement Strategy and Governance)

Wannan saƙon an aika shi ne a madadin Board Selection Task Force da Kwamitin Zaɓuɓɓuka