Kamar yadda UNICEF ta sanar, kusan fiye da rabin kananan yara na duniya suna fuskantar cutarwa mai tsanani. An ƙiyasta cewa, kaso 64 na waɗannan kananan yara suna zaune a ne a yankin kudancin Asiya. Har wayau a acikin wannan ƙasida, an ƙara bayyana cewa ba wadanda aka cutar ba kaɗai, har wadanda suka ga yadda ake cutarwan, ,hanya mafi a'ala shine a gusar da wannan cutarwar. Amma kuma abun lura ne da a matsayin sashin kundin ilimi, wato encyclopedia, babu wani mataki da aka dauka don kawo ƙarshen wadannan cin zarafi na kananan yara a tsakanin al'ummomin Wikipedia. Saboda haka, a karo na farko muna ƙoƙarin shirya gangami na Wiki loves Children a Wikipedia ta Bengali da Wikibooks. Kamar sauran littatafai ba wikibooks, Wikibooks na Bengali suna da project na yara wanda ake kira Wikijunior, amma a halin yanzu kusan basu aiki. Saboda haka, mun kara shi a cikin project din da kokarin bunkasa ta da kara mata mahimmanci a wajen koyarwar yanar gizo don kananan ɗalibai masu tasowa. Musamman a wannan lokaci na cutar Covid-19 inda zata taka muhimmin rawa wajen koyarwa ta yanar gizo kuma zamuyi ƙoƙarin tsara Wikibooks (musamman Wikijunior) don ya zama abokin koyar da yara a maimakon Wikipedia.
|