This page is a translated version of the page Wikiquote and the translation is 96% complete.

"Wikiquote" matattara ce a kan yanar gizo wadda take ɗauke da maganganun fitattun mutane cikin harsuna daban daban. Ana fitar da duk abun ciki amma maganganun haƙƙin mallaka suna a ƙarƙashin GFDL da CC-BY-SA a cikin iri ɗaya kamar yadda sauran ayyukan Wikimedia Foundation.

Tambarin Wikiquote
Tambarin Wikiquote

Farawa

Ta fara daga a post da Fonzy a ranar June 27, 2003.

tunani da aka kawo: Wikiquotionary Ensakulifidiya ta Zantuttuka (quotes). Za'a iya samo shafin temp [$temp-shafin gida a nan] - fonzy.

Ta fara a matsayin quote.wikipedia.org a ranar 10 ga watan Yulin, 2003 sannan daga baya ta samu shafin ta a, wikiquote.org a ranar 25 ga watan Agustan, 2003.

Bunkasawa

Wikiquote tana da zantuttuka fiye da mukalai 2,500 a cikin yaruka guda hudu a shekara ta 2004, shekara daya bayan an bukaci bude ta a karkashin shafin wikiquote.org. Wasu masu magana da harsuna wanda ba Turanci ba sun bukaci na su shafukan sannan a ranar 17 ga watan Yuli, an ƙirƙire su, aka fara Wikiquote a harsuna kamar Jamusanci, Faransanci, Italiyanxi da kuma Folish.

Wikiquote na kara fadada a hankali amma yadda ya kamata. A karshen watan Satumba akwai akalla Wikiquotes guda 15, manya da ƙanana. A ranar 1 ga watan Disemba, an samu shafukan Wikiquote guda 24. Akwai akalla mukalai 6,500 gaba daya a Disemban shekara ta 2004. A karshen watan Mayun 2005 daukakin yawan mukalan sun kai 14,000. Ta kunshi mukalai 30,000 a cikin harsuna fiye da 30 a cikin watan Febrerun 2006, fiye da mukalai 60,000 acikin harsuna 87 a cikin watan Mayun 2007 sannan kuma fiye da mukalai 80,000 acikin harsuna 89 acikin watan Yunin 2008.

Tun daga update na karshe acikin watan Yunin 2008, adadin yawan harsuna sun tsaya cak, a yayinda adadin mukalai suka ninka. Ya zuwa watan Mayun 2014, akalla shekaru goma sha daya bayan ƙirƙirar ta, shafin na Wikiquote a yanzu ya kunshi akalla muƙalai 168,000 acikin harsuna 89. Shafunkan harsuna gua ashirin da takwas na da fiye da mukalai 1000. Shafukan harsuna guda hamsin da shida na da mukalai 100 ko miye da hakan.

Shafukan Wikiquote mafiya girma sune na harsunan Italiya da Ingilishi, tare da mukalai fiye da 48,000 da 46,000 a jere. Na uku shine Wikiquote na mutanen Foland, da ke dauke da mukalai fiye da 24,000.

Ƙalubale

Wasu lokutan shafukan Wikiquote suna fuskan ƙalubale da matsaloli. Daya daga cikin fitattun ƙalubalen sune matsalolin haƙƙin mallaka (copyright) a shafukan Wikiquote na Faransanci. Don magance matsalolin, acikin watan March na 2006 Gidauniyar da yanke shawarar sauke shi kasa, goge duk wasu bayanai da kuma sake ƙaddamar da su.

Ko yaya, editoci masu jajircewa sun shawo kan matsalar. Sun sassan yarjejeniyar su da ƙa'idojin su, sannan kuma an sake ƙaddamar da French Wikiquote a ranar 4 ga watan Disemban 2006.

Ƙididdiga

Duba Ƙididdigar Wikimedia – Wikiquote

An cire teburi daga Wikiquote/Table.

Muhimman ababen tunawa

Muhimman yawan mukalai da ake tunawa 100, 500, 1k, 2k, 5k an kara zuwa 50k, 10k an kara zuwa 100k, 25k an kara zuwa 250k, 50k an kara zuwa 500k, sannan kuma 100k zuwa 1000k.

Har wayau an bukaci sanarwa a Wikimedia News

Ana iya samun muhimman abubuwan tunawa a archives.

2024

2023

2022

2021

2020

2019

2015

2013

2012

2010

2009

An kirkiri Alemannic Wikiquote a daban a tsakanin Alemannic Wikipedia: Alemannischi Spruchsammlig (Wikiquote).

Sabon Wikiquote

Idan kuna so ku kaddamar da Wikiquote a harsunan da kuke so, kuna iya neman izini, da cike wasu bukatu. Duba Requests for new languages don neman karin bayani.

== Sadarwa a tsakanin-daukakin Shafuka

Yawancin shafuka harsuna na Wikiquote suna da wuraren tattaunawa akan wikis din su. Idan yana baka wuya wajen nemo su, ku yi kokarin tattaunawa akan: Kowanne shafi na wiki.

Wikiquote da duniya baki daya na gudanar da wasu shafukan tattaunawan.

Shafuka masu alaƙa

Tsarin Wikiquote

Tarihi

Ƙasidu