Zaɓukan Gidauniyar Wikimedia/2022/Tsare-tsaren cancantan mai kaɗa kuri'a

This page is a translated version of the page Wikimedia Foundation elections/2022/Voter eligibility guidelines and the translation is 100% complete.

Cancantan kaɗa kuri'a

Babban ƙa'ida

Kada a kulle ku a fiye da manhaja ɗaya dan samun yin zaɓe.

Editoci

Kuna iya kaɗa kuri'ar ku daga duk wani akwant ɗin ku ɗaya da kuka yi rijista da shi a Wikimedia wwiki. Zaku iya kaɗan kuri'a sau ɗaya ne kacal, koda ko akwant nawa kuke da shi. Dan cancanta, akwant ɗin zaɓen ɗaya dole ya kasance:

  • kada a kulle ka a manhaja fiye da ɗaya;
  • kuma kai ba robot bane;
  • kuma kayi a ƙalla gyararraki 300 kafin 5 Yuli 2022 a dukkanin Wikimedia wikis;
  • kuma ka yi a ƙalla gyararraki 20 daga tsakanin 5 Janairu 2022 da 5 Yuli 2022.

AccountEligibility tool za'a iya amfani da shi dan tabbatar da cancantan mai kaɗa kuri'a.

Developers

Developers sun cancanci kaɗai kuri'a idan:

  • su Wikimedia server administrators ne tare da izinin shell access
  • ko sunyi a ƙalla maja ɗaya na wani gyara zuwa Wikimedia repos akan Gerrit, a tsakanin 5 Janairu 2022 da 5 Yuli 2022.

Ƙarin ma'auni

  • ko yayi a ƙalla maja ɗaya na gyara zuwa repo dake cikin nonwmf-extensions ko nonwmf-skins, tsakanin 5 Janairu 2022 da 5 Yuli 2022.
  • ko yayi a ƙalla maja ɗaya na gyara zuwa duk wani kayan aikin Wikimedia repo (misali magnustools) tsakanin 5 Janairu 2022 da 5 Yuli 2022.
  • ko kuma a ƙalla ya yi gyara 300 kafin 5 Juli 2022, da kuma gyara 20 a tsakanin 5 Janairu 2022 da zuwa 5 Juli 2022, a Translatewiki.
  • ko kuma ya kasance mai kula/bada gudummawa a duk wani kayan aiki tools, bots, user scripts, gadgets da Lua modules akan Wikimedia wiki
  • ko kuma yayi aiki sosai wurin shiga cikin zane/ko kuma sake duba tsarin gudanar da bunƙasa fasaha da ya alaƙanci Wikimedia.

A sani: idan ka cimma babban ma'aunin, zaka iya kaɗa kuri'a kai tsaye da sauri. Dangane da wasu iyaka ta fasaha da Securepoll ke da shi, mutanen da basu cimma ƙarin ma'aunan da aka bayar ba, ba zasu iya jefa kuri'a kai tsaye ba, sai dai idan sun cimma wasu daga cikin sauran ma'aunan cancantan. Idan kana tunanin ka cimma sauran ƙarin ma'aunan cancantan, turo mana da saƙo ta email a board-elections lists wikimedia org da dalilai cikin a ƙalla kwanaki 4 kafin ƙarshen ranar zaɓe wato, a ranar ko kafin 2 ga watan Satumba 2022. idan ka cimma cancantan, to zamu sanya ka cikin jerin waɗanda zasu yi da kanmu, don ka sama daman kaɗa kuri'a.

Ma'aikatan Gidauniyar Wikimedia da ƴan kwangila

Ma'aikata da ƴan kwantiragi na Gidauniyar Wikimedia na yanzu, zasu iya zaɓe idan an ɗauke su aiki daga Gidauniyar tun daga 5 Yuli 2022.

Ma'aikatan rassa na tafiyar Wikimedia da ƴan kwantaragi

  • Ma'aikatan reshunan Wikimedia na yanzu, ƙungiyoyin tematik da ƙungiyoyin masu bada gudummawa da ƴan kwangila sun cancanci zaɓe idan an ɗauke su aiki a ƙungiyoyinsu daga 5 Yuli 2022.
  • Mambobin ƙungiyoyi na ƙa'ida kamar yadda aka lissafa a cikin dokoki na Reshunan Wikimedia a yanzu, ƙungiyoyin tematic ko ƙungiyoyin masu bada gudummawa sun cancanci yin zaɓe idan sun fara aiki a wannan wuraren faga 5 Yuli 2022

Kwamitin Ƙungiyoyin da aka yi Alaƙa da su da Kwamitin Zaɓe zasu tabbatar da jerin Kungiyoyin Alaƙa da suka cancanta kafin 1 Augusta 2022.

Membobin Amintattu na Gidauniyar Wikimedia da membobin Mashawarta

Na yanzu da tsoffin mambobin Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Wikimedia da Mashawarta na Gidauniyar Wikimedia.

Membobin Kwamitin Tafiyar Gidauniyar Wikimedia

Mambobin Kwamiti na yanzu na Tafiyar Wikimedia sun cancanci zaɓe idan sunyi aiki a wannan maƙaman daga 5 Yuli 2022.

Kwamitin Zaɓe zai fitar da jeri na waɗanda suka cancanta daga Kwamitin Tafiyar Wikimedia kafin 1 Augusta 2022.

Masu shiri a Tafiyar Wikimedia na Al'umma

Masu shiri da basu da matsala, waɗanda basu cancanci kaɗa kuri'a ba ƙarƙashin wasu rukunnai, sun cancanci zaɓe idan sun haɗa ɗaya daga cikin waɗannan:

  • sun tura buƙatar nema, sun karɓa da yin rehoto akan a ƙalla wani tallafi na Gidauniyar Wikimedia tun a 1 Satumba 2021.
  • a inda mai shiri na a ƙalla hackathon da aka yi tallafi, gasa ko wani shiri na Wikimedia da samar da kundin bayanai akan-wiki da a ƙalla masu halarta/maziyarta/masu shiga 10 tsakanin 5 Janairu 2022 da 5 Yuli 2022.

Ƙarin ma'aunan cancanta

Idan kana ganin kana da cancantan da aka ƙara, yi hakuri ka tura saƙo zuwa ga board-elections@wikimedia.org tare da dalilan ka a ƙalla kwana huɗu kafin ranar ƙarshe na kaɗa kuri'a i.e. a ko 2 Satumba 2022. Idan ka haɗa cancantan, zamu sanya ka a jerin wanda zasu yi zaɓen, dan samun kaɗa kuri'a.