Zaɓukan Gidauniyar Wikimedia/2022/Sanarwa/Jawabai da aka samar na Kamfas ɗin Zaɓen 2022

Samar da jawabai a Kamfas ɗin Zaɓen 2022

Kuna iya samun wannan saƙon an fassara zuwa ƙarin wasu yaruka akan Meta-wiki.

Barkan mu,

Masu sakai a Zaɓen Kwamitin Amintattu na 2022 ana gayyatar ku da ku gabatar da jawabai da za'a yi amfani da su a Kamfas ɗin Zaɓen.

Kamfas ɗin Zaɓe wani kayan aiki ne da zai taimaka wa masu kaɗa ƙuri'a zaɓan ƴan takara da suka dace da abinda suka yarda da shi kuma suke tunani. Mambobin al'umma zasu gabatar da jawabai dan ƴan takara su amsa ta amfani da Lickert scale (agree/neutral/disagree). Amsoshin da ƴan takaran suka bayar na jawaban zai shiga cikin kayan aiki na Kamfas ɗin Zaɓen. Masu kaɗa ƙuri'a zasu yi amfani da kayan aikin ta sanya amsar su ga jawaban da ɗaya daga waɗannan (agree/disagree/neutral). Sakamakon zai nuna ɗan takara da yafi dacewa da abin da mai kaɗa ƙuri'a yake so ko yafi yarda da shi.

Wannan ne lokutan da za'a gudanar da Election Compass:

Yuli 8 - 20: Masu Aikin Sakai zasu gabatar da jawabai dan Election Compass

Yuli 21 - 22: Kwamitin Zaɓe zasu bincika jawaban dan tantancewa da fitar da jawaban da basu dace ba

Yuli 25 - Augusta 3: Masu Aikin Sakai zasu yi zaɓe akan jawaban

Augusta 4: Kwamitin Zaɓe zasu zaɓi jawabai 15 da suka fi cancanta

Augusta 5 - 12: ƴan takara zasu rinjayar da kawunan su tare da jawaban

Augusta 16: Za'a buɗe Election Compass dan masu kaɗa ƙuri'a su yi amfani da shi dan taimaka masu yin tunani

Kwamitin Zaɓe zasu zaɓi jawabai mafi cancanta 15 a farkon Augusta. Kwamitin Zaɓe zasu lura da gudanarwan, da taimakon tawagar Tsarin Gudanarwa da Shugabanci (Movement Strategy and Governance team). MSG zasu bincika su ga tambayoyin suna daidai, babu maimaici, babu kurakurai, da sauran su.

Da alkhairi,

Tsarin Gudanarwa da Shugabanci (Movement Strategy and Governance)

Wannan saƙon an aika shi ne a madadin Board Selection Task Force da Kwamitin Zaɓuɓɓuka