Hukumar Bunkasa Shugabanci/Sanar akan Kira don yin Sharhi
Outdated translations are marked like this.
Hukumar Bunkasa Shuwagabanci: An yaba da ra'ayoyin ku
Kungiyar bunkasa al'ummomi na Wikimedia Foundation bada tallafi don samar da hukumar da zata bunkasa shuwagabanci a tsakanin kungiyoyi daban daban na duniya. Manufar hukumar shine bada shawarwari don inganta harkokin shugabanci.
Kungiyar na neman sharhi akan nauyi da ya jibanci Hukumar Bunkasa Shugabanci. Wannan shafin yana yada shawarar Leadership Development Task Force da kuma yadda zaku iya bada gudummawar ku. Za'a amsa sharhi akan shawarar a tsakanin 7 zuwa 25 ga watan Fabrairu 2022.