Kwamitin Zaɓen Gidauniyar Wikimedia/Tantancewa/2023/Sanarwa - sabbin membobi
Sanar da sababbin membobin kwamiti
Barkan ku na nan,
Muna farin cikin sanar da kwamitin sababbin membobin da mashawarta. Kwamitin Zaɓe yana taimakawa tare da tsarawa da aiwatar da tsari don zaɓar amintattun Zaɓaɓɓun Al'umma da Ƙungiyoyi don Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Wikimedia. Bayan an gudanar da zabukan fitar da gwani, ƴan takarar da suka fi kowa ƙarfi sun tattauna da hukumar inda aka bukaci ƴan takara hudu su shiga kwamitin zaben. An bukaci wasu 'yan takara huɗu su shiga a matsayin masu ba da shawara.
Godiya ga daukacin waɗanda da suka gabatar da sunayensu don tantancewa. Muna sa ran yin aiki da kwamitin zabe nan gaba kadan.
A madadin Kwamitin amintattu na Gidauniyar Wikimedia,