Manhajin Wikimedia Foundation Board of Trustees/Kira don jin tsokaci: Zaben Kwamitin Amintattu (Board of Trustees)

Matsalar da za'a warware

Manhajan Wikimedia Foundation da harkokinsu sun habaka a tsakanin shekaru goma da suka wuce, haka zalika wannan hukumar ta kasance yadda take fuskar tsari da harkoki, sannan kuma karancin wakilci daga sassa daban daban na duniya ya zama daya daga cikin ababan la'akari.

A cikin shekara ta 2021, an tattauna wasu daga cikin wadannan matsaloli a lokacin kira na musamman don tattaunawa akan hukumar amintattun wikimedia foundation wato Call for Feedback: Community Board seats. An kaddamar da kuduri akan zaben watau 2021 Board of Trustees election included updated practices don shawo kan bukatun wannan hukumar. Anyi amfani da tsarin "single transferable voting" don kara bada daman wakilci a wannan manhajan daga sassa daban daban. Amintattun sun sanar da kwarewarsu sannan suma 'yantakara sun sanar da nasu kwarewar don masu zabe su san su. Anyi amfani da kafafe daban daban da harsuna don samar da 'yantakara da masu jefa kuri'u daga kungiyoyi daban daban ta hanyoyin sadarwa iri-iri.

Muna fatan gano wasu karin mafita don dubin hanyoyin habaka cigaban wannan hukuma a yayin wannan kira na samun tsokaci na shekara ta 2022. Bugu da kari, muna so muyi amfani da wannan dama don fahimta daga al'ummomi akan yadda sukayi cudanya da 'yantakara a lokacin harkokin zaben.

Tsarin kira don tsokaci

Da wannan kira don samun tsokaci, zamu dauka hanyoyi daban daban don samun tsokaci daga al'ummomi daga al'amurran shekara ta 2021. A maimakon jagoranci da shawarwari, wannan kira zai ta'allaka akan muhimman tambayoyi. Manufar shine a habaka tattaunawa na gabaki daya da kuma hadin kai wajen cigaban shawarwari

Mun gode da lokacin da ka/ki dauka don bada gudunmawa a wannan kira na samun tsokaci da kuma taimkawa wajen samun karin wanzuwa da kuma kyakyawar ayyuka na Hukumar amintattu "Board of Trustees"

Muhimman tambayoyi

  1. Wani hanya ne mafi a'ala don tabbatar da wanzuwar wakilci a tsakanin 'yantakara?
  1. Menene ababen da ake bukata daga 'yantakara a lokacin zabe?
  1. How should affiliates participate in the elections?

Yi bayani akan tambayan nan

Yadda zaku shiga

Movement Strategy and Governance Stategy and Governance ma'aikatan suna iya tallafawa tattaunawa a cikin yaruka da yawa. Ana maraba da tattaunawa a kowane harshe, kodayake muna iya buƙatar dogara ga masu fassara na sa kai don taimakawa taƙaita harsunan da ba mu da su a cikin ma'aikata. Kuna iya samun hanyoyin haɗin kai zuwa tattaunawa a cikin yaruka da yawa a cikin tebur akan Tattaunawa Maɓallin Tambayoyi shafi. Kuna iya samun tattaunawa akan Tattaunawar zaɓi na Telegram Board. A tuntuɓi mai gudanarwa a yankinku don tsara tattaunawar al'umma ko ba da amsa.

Tsarin lokaci

  • 23 Disamba: Sanarwa na Kira don Saurara
  • 10 ga Janairu: Kira don amsawa yana buɗewa
  • 16 ga Fabrairu: Kira don amsawa yana rufe
  • 26 Fabrairu: Buga rahoton ƙarshe na Kira don Sake amsawa

Kowace mako ƙungiyar Dabarun Harka da Gudanarwa za ta buga report weekly don ɗaukar ra'ayoyin da tattaunawa da ke faruwa a cikin makon da ya gabata.

Bayani mai fa'ida

Kwamitin Amintattu ita ce hukumar gudanarwa na Wikimedia Foundation, ƙungiyar ma'aikata +450 da ke tallafawa ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa waɗanda ɗaruruwan ayyuka, al'ummomi, da alaƙa suka kafa. Aikin hukumar shi ne kula da gudanarwar gidauniyar Wikimedia. Wannan ya haɗa da:

  • Shiga cikin kafa dabarun dogon lokaci na Wikimedia Foundation.
  • Sa ido kan ayyuka da kudade don tabbatar da cewa kuɗi suna da lafiya, daidai da manufa kuma suna bin wajibai na doka.
  • Hayar, sarrafawa, ba da shawara, da saita diyya ga Shugabar Gidauniyar Wikimedia.

Ana samun ƙarin bayani a cikin Board Handbook.

Duba kuma