Watan Al'adun Diflomasiyyar Kasar Ukraine
Watan Al'adun Diflomasiyyar Ƙasar Ukraine gasa ne na rubuta mukalai da suke mayar da hankali wajen sanya al'adu na kasar Ukraine a Wikipedia a harsuna daban-daban, wanda ƙugiyar Wikimedia ta Ukraine ke shiryawa dangane da hadin gwiwar Ukrainian Institute da kuma ma'aikatar kula da harkokin waje wato Ministry of Foreign Affairs of Ukraine.
![](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/c/c8/UEWikipedia.png/250px-UEWikipedia.png)
Dalilin gudanar da wannan gangami na Watan al'adun Diflomasiyyar ƙasar Ukraine shine don tattara da rarraba bayanai dangane da al'adu da fitattun mutanen ƙasar Ukraine a harsuna da dama na Wikipedia don kara yawa da ingancin yaduwar ilimi na kyauta dangane da kasar Ukraine ga duniya baki daya. Akwai darussa da dama da babu su a Wikipedia, sannan ta wannan gasa ne, masu bada gudunmawa zasu iya inganta mukalai akan al'amurran al'adun gargajiya masu muhimmanci ga mutanen Ukraine zuwa wasu harsuna