Ilimi/Labarai/Janairu 2022
Wannan watan akan Ilimantarwa
Sauti 11 • Abubuwan lura 1 • Janairu 2022
Abubuwan da suka kunsa • Kanun labarai • Yi rijista
Gasar rubutun mukalai na sa'o'i 30 a Estonia ya haɗa da ƙungiyoyi 10 da mahalarta 33. Gabaɗaya sun rubuta cikakkun labarai guda goma. Kungiyar da ta yi nasara ta samu Yuro 1000. Kara nazari… Hotuna da labaran da aka bayar a cikin aikin 'Cieszyn Silesia a cikin Wikipedia' yanzu za'a iya ganinsu Kara nazari… Gasar WikiChallenge na makarantun Afurka gasane na rubuce-rubuce da aka keɓe wa ɗalibai masu kimanin shekaru 8-13 kuma wacce ke gudana a ƙasashen Afirka da yawa na Faransanci. An ƙaddamar da shi a cikin 2017, yanzu ya rufe bugu na 3 tare da labarai 138 da aka buga akan Vikidia da hotuna sama da 800, zane da bidiyo waɗanda yaran suka shirya kuma aka shirya a Wikimedia Commons. Kara nazari… A cikin Oktoba 2021, ƙungiyar Ilimi a Gidauniyar Wikimedia ta yi maraba da rukunin farko na wikimedians zuwa Horarwar Masu Koyarwa don "Karanta Wikipedia a cikin Aji". Taya murna ga Wikimedians 22 da suka kammala ToT kuma yanzu suna shirye don taimakawa ƙarin malamai a ƙasashensu don amfani da Wikipedia azaman kayan aikin koyarwa! Kara nazari…
|
|
Taron Wiki na shekara-shekara kashi na 9 zai gudana (ta yanar gizo) a ranar 25 ga Afrilu a zaman wani ɓangare na Taron Yanar Gizo na 2022. Kara nazari… Halarci Makon EduWiki, ku kasance da tare damu, sami damar haɗin gwiwa, sannan ku yada albarkokin da Wikimedia ke kawowa ga ilimi. Kara nazari… Joyce De Guzman ta ba da labari game da gwagwarmayarta, jin daɗi, da buri game da horo da ayyukan Wiki acikin ɗan takaitaccen hira. Kara nazari… Dalibai sun wadatar da Wiktionary na Ibrananci tare da maganganun Littafi Mai-Tsarki waɗanda ake amfani da su a cikin Ibrananci na zamani Kara nazari…
|